Saturday, July 13
Shadow

YANZU-YANZU: Babiana Ta Fitar Da Takardar Saki Ukkun Da Mìjinta Yayi Mata

DAGA Shafin Dokin Karfe TV

Jarumar Tik-Tok Hafsat Waziri, wadda aka fi sani da Babiana ta bayyana cewa mijinta ya sake ta saki uku dan haka, yanzu haka ba ta da aure kuma ta ga cewa bai kamata ta yi ta ɓoye-ɓoyen sakin da mijinta yayi mata ba gara ta fito ta shaidawa Duniya halin da take ciki.

Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu takardar shaidar sakin wadda Babiana Waziri ta aiko mata inda a ciki aka bayyana cewa “Ni Muhammad Izzudden Eze na saki matata saki uku”. An rubuta takardar ranar 11 ga watan 4 na shekarar 2024, kamar yadda kuke gani.

Karanta Wannan  Ji yanda wata mata ta laftawa mijinta tabarya akai ya mutu bisa zargin cin amanarta da matan banza da yake yi

Babiana ta kuma bayyana cewa “Na shiga bala’in rayuwa a dalilin aurensa da nayi, har asibitin mahaukata an kai ni a dalilin aure kuma har yanzu ban gama farfaɗowa ba”. In ji ta.

Daga nan ta ƙara da cewa “Mijina ba ya biya mun buƙatuna na rayuwa ya bar ni, ni nake yi wa kaina komai. Ba daidai ba ne ka auri mata ba ka da kuɗin ciyar da ita da biya mata buƙatunta ba”. In ji ta.

Ta kuma ta ƙara da cewa “Na godewa Allah da jarrabawa ta ta zo a aure. Ni na yi aure don in raya Sunnar ma’aiki amma abin ya zame mun masifa da bala’i”. A cewarta.

Karanta Wannan  WATA SABUWA: Sai Da Na Auri G-Presh Na Gane Cewa Shi Ba Nàmìjì Ba Ne A Zamantakewar Aure, Cèwar Sayyada Sadiya Haruna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *