fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Yanzu-Yanzu: Babu ranar bude jami’o’in Najeriya>>ASUU

Sama da watanni 2 da yajin aikin kungiyar malaman jami’a ta ASUU, kungiyar tace babu ranar bude jami’o’in kasarnan.

 

Shugaban ASUU reshen jihar Kano, Abdulkadir Muhammad ne ya bayyana haka a jiya.

 

Yace bude jami’o’in ya ta’alaka ne ga shirin gwamnatin tarayya na biya musu bukatunsu.

 

Yace muddin gwamnati bata biya musu bukatunsu ba, a shirye suke su ci gaba da yajin aikin.

 

Yace gwamnatin ba da gaske take ba wajan biyansu hakkokinsu.

 

Yace gwamnati bata zuba jari a bangaren ilimi duk da yake cewa babu bangaren da ya kai ilimin muhimmanci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.