Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zabe mai zuwa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ziyarar daya kaiwa shugaban kasar, Muhammadu Buhari a mahaifarsa ta Daura ranar lahadi.
Wanda hakan ya tabbatar da maganar gwamnan jihar Kano, Ganduje wanda yace Tinubu ya amince ya zabi Musulmi a matsayin abokin takararsa.
A baya Tinubu ya zabi Ibrahin Masari a matsayin abokin takararsa na wucin gadi, kuma yanzu yayi murabus yace zai taimakawa kasar ta fannin.