Rahotanno daga jihar Rivers na cewa Wasu bata gari sun saka Bam a cocin mahaifin gwamnan Jihar, Nyesom Wike dake babban birnin jihar, Fatakwal.
Rahoton wanda TheNation ta kawo yace wanda suka kai harin su 5 ne inda suka shiga cikin cocin me suna Christian Universal Church International da yammacin jiya, Asabar inda suka saka ababen fashewar wanda ake tsammanin nakiyoyine.
Tashin bam din ya lalata cocin sosai, a cewar Rahoton wanda hakan ya matukar saka fargaba a zukatan mutanen yankin.
Babu dai wana kungiya data dauki alhakin abin amma an kama 2 daga cikin wanda suka kai harin inda aka mikasu hannun ‘yansanda.