Kungiyar Chelsea tayi wuff da zakaran gwajin Manchester City watau Raheem Sterling.
Sterlinga ya bar Manchester City ne bayan ya kasance a kungiyar na tsawon kakanni bakwai,
Kuma yayi nasarar lashe kofuna bakwai a kungiyar wadda ya koma tun yana dan shekara 20.
Sannan Sterling ya kasance dan wasa na farko da sabon mai kungiyar Todd Boehly ya saya.