Labarin da muke samu da dumi-dumi na cewa gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.
Kwamishinan yada labarai na jihar, John Okiyi Kalu ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai da safiyar yau, Litinin.
Yace gwamnan ya killace kansa kuma ya bukaci magaimakinsa daya ci gaba da kula da al’amuran mulki har sai abinda hali yayi.