Daga Comr Abba Sani Pantami
Idan baku manta ba, da farko kungiyar malaman jami’o’in kasar ASUU ta shiga yajin aikin gargadi har na tsawon wata guda inda daga bisani ta kara tsawaitawa har na watanni biyu.
A yau Litinin wa’adin watanni uku ya kare, inda ake tunanin kungiyar za ta iya janye yajin aikin nata, duba da gwamnatin kasar ta bada umurnin a bawa kungiyar Biliyan 465 don inganta Jami’o’in kasar, wanda yana daga cikin manyan dalilan da yasa kungiyar take yajin aiki lokaci bayan lokaci.
A yau kwatsam sai kungiyar ta sake fitar da jawabin cewa ta kara tsawaita yajin aikin nata, har na tsawon watanni ukku, domin gwamnatin kasar ta samu damar cika mata dukkannin bukatunta da suka hada da alawus-alawus din malamai da amincewa da tsarin biyan su albashi a karkashin tsarin UTAS madadin tsarin IPPIS na gwamnatin kasar.
Bayan wannan sanarwar kennan wasu dalibai a jihar Legas suka fantsama zanga-zanga a wasu sassan jihar. Tun tuni dama daliban kasar sun yi barazanar barkewa da zanga-zanga a fadin kasar ko da kuwa zasu rasa rayukan su.