Shahararren dan majalisar dokokin Najeriya kuma mai yawan cece-kuce, Sanata Dino Melaye ya sha kaye a yunkurinsa na komawa majalisar dattawan Najeriya bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a jihar Kogi.
Wakilan mazabar sa, mazabar Sanatan Kogi ta Yamma sun zabi abokin takarar sa Hon. Tajudeen Yusuf wanda aka ce ya kasance mai biyayya ga Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.
Dino Melaye ya samu kuri’u 99 ne kawai yayin da abokin hamayyarsa Yusuf mai wakiltar mazabar Kabba/Bunu Ijumu a majalisar wakilai ya samu kuri’u 163.
An sake fafatawa ne bayan dukkan masu neman tsayawa takara sun samu kuri’u 88 kowanne a ranar Litinin.
Amma a sake zaben da aka yi a ranar Talata, Tajudeen Yusuf (TJ) ya samu rinjayen kuri’u.
Dino yace ya amince da rashin nasarar da yayi amma yana zargin delegates ne suka hade masa kai.