YANZU-YANZU: Gobara Ta Tashi A Dakin Kwanan Dalibai A Jami’ar Dan Fodiyo Dake Sokoto
Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)
Dakin kwanan dalibai mai suna Benji ya kama da wuta a yau Juma’a, inda aka yi asarar abubuwa da dama adalilin wannan gobara.
Daya daga cikin wakilinmu Abdulnasir Yusuf Ladan ya zanta da wani dalibin makarantar wanda gobarar ta faru a gaban shi mai suna Musa Yusuf Mahogany, dalibin ya shaida mana cewa wutar ta tashi ne a daidai lokacin da ake sallar Juma’a.

Dalibin ya kara da cewa wutar ta kara fusata ne a dalilin akwai tukunyar gas da risho da dama a dakin kwanan, hakan ya sa gobarar ta ci sosai.
Haka kuma ya kara bayyana ma wakilin mu cewa a daidai lokacin da wutar ke tsakiyar ci, sai ga motar ‘yan kwana-kwana cikin gaggawa, ba a yi wata-wata ba suka kashe wutar.