Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya shiga jerin masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.
Tawagar wasu fulani daga Arewa ne suka saiwa Goodluck Jonathan wannan fom din.
Zuwa yanzu dai, Goodluck Jonathan bai bayyana aniyaraa ta son tsayawa takarar shugaban kasa ba.
Abin jira a gani shine zai amince da wannan fom din da aka sai masa, sannan kuma zai bar jam’iyyar PDP zuwa APC?
