fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Jihar Nasarawa na ganawar Sirri da Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari Da Gwamnan jihar Nasarawa, Mista Abdullahi Sule, suna ganawa a halin yanzu.

 

Sule ya isa fadar Shugaban kasa da misalin karfe 10 na safe gabanin taron majalisar zartarwa ta tarayya.

 

Ba a san dalilin ganawar da gwamnan da shugaban kasa Buhari keyi ba.

 

Nasarawa ita ce jihar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yake, wanda Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya sauke shi a ranar Litinin.

 

Binciken da aka yi ya nuna cewa mai yiwuwa gwamnan ya ziyarci Fadar Shugaban Kasa don yin bayani ga Shugaban kasa kan halin da ake ciki na tsaro a cikin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.