fbpx
Friday, July 1
Shadow

Yanzu-Yanzu: Gwamnati na shirin bude makarantun gaba da sakandare

Rahotanni sun bayyana cewa duk da yawan masu cutar Coronavirus/COVID-19 a Najeriya ya tasamma mutane Dubu 50, Gwamnatin tarayya na shirin sake bude makarantun gaba da sakandare.

 

Hakan ya bayyanane a yayin da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha kewa ‘yan Najeriya bayani akan cutar a Jiya, Litinin. Hutudole ya samo muku cewa Boss Mustapha ya bayyana farin cikinsa kan yanda aka fara jarabawar WAEC kuna daliban Najeriya sun samu damar rubuta jarabawar.

Boss Mustapha ya bayyana cewa gwamnati na lura da yanda ake ci gaba da samun raguwar masu kamuwa da mutuwa sanadiyyar cutar duk da cewa yawan masu cutar a Najeriya ya tasamma Dubu 50. Hutudole ya ruwaito Boss Mustapha na cewa, suna sane da kiraye-kirayen da ake ta bangaren Ilimi wanda yace Ilimi na daya daga cikin abubuwan da gwamnati ke baiwa Muhimmanci.

Karanta wannan  Hukumar zabe ta INEC ta karawa masu yin rigistar katin zabe lokaci amma ta gargadi jam'iyyar APC, PDP da dai sauran su

 

Ya kuma tabbatar da cewa, suna duba yiyuwar sake bude makarantun gaba da sakandare nan ba da jimawa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.