Hadakar Rundunar tsaro da ake kira da MNJTF sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram me suna Abubakar Dan-Buduma.
Hadakar sojojin kasa dana sama ne suka kashe Abubakar Dan-Buduma da mayakansa a kauyen Kwalaram dake karamar Hukumar Marte ta jihar Borno.
A watan Janairu da ya gabata ne dai kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram ta bayyana cewa, ta nada sabbin Shuwagabannin ta, kuma Abubakar Dan-Buduma na daga cikin wanda aka nada din.
Amma yanzu kashi jami’an tsaro sun samu nasarar kasheshi.