fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yanzu-Yanzu: Hotunan farko na sabon shugaban ma’aikatan Buhari a wajan taron majalisar zartaswa a yau

Sabon shugaban ma’aikatan shugaba Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari kenan a wadannan hotunan a taron majalisar koli na farko daya halarta a fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

 

Tun a jiyane dai labaru suka karade shafukan sada zumunta cewa an nada Gambari sabon shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasar.

 

Gambari dai dan Asalin jihar Kwara ne wanda kuma tuni sarkin kwarar ya fito yawa shugaba Buhari godiya kan wannan nadi.

Gambari ya gaji Abba Kyari wanda ya rasu sanadiyyar cutar Coronavirus/COVID-19.

A yau ma an yi amfani da fasahar sadarwar zamani wajan zaman.

Leave a Reply

Your email address will not be published.