Hukumar ‘yan sanda a jihar Legas ta damke wasu jami’ai da suka yi kokarin hana zanga zangar da ‘yan kungiyar kwado keyi kan yajin aikin ASUU.
Jami’an sun dakatar da ‘yan kungiyar kwadagon ne ta NLC akan titi wanda hakan yasa suka fara cacar baki a tsakaninsu,
Daga bisani hukumar ‘yan sanda ta dauke jami’an ta kaisu ofishinta yayin da su kuma ‘yan kungiyar kwadagon suka cigaba da zanga zangar tasu.
A yau ne kungiyar ta kwadagon ta cika alkawarin datayi na zanga zanga kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in Najeriya keyi tun watan Febrairu.