YANZU-YANZU: Innalillahi wa’innalaihi raji’un, Dan takara ya mutu a hanyar komawa gida bayan yaje ya biya kudin fom din takararsa
Daga Muryoyi
Allah ya yiwa Hon. Sale Ahmadu Bawa rasuwa dan takarar majalisar dokoki ta jiha mai wakiltar mazabar Warji a jihar Bauchi.
Muryoyi ta ruwaito margayin ya rasu ne a sakamakon hadarin mota da ya rutsa dashi a yammacin yau akan hanyarsa ta komawa gida bayan yaje banki ya biya kudin sayen fom din takararsa a karkashin jam’iyyar PRP.