fbpx
Monday, August 15
Shadow

Yanzu-Yanzu: JAMB ta kayyade makin shiga jami’a

Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB ta kayyade 140 a matsayin makin shiga jami’un gwamnatin tarayya a shekarar 2022.

 

JAMB ta kayyade makin ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ta yi.

 

Sannan ta kayyade maki 100 wanda kwalejojin ilimin tarayya dana Kimiyya da fasaha zasu yi amfani dasu wajan daukar dalibai.

 

Jami’in hukumar, Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka amma yace kowace jami’a na da damar kayyade makinta amma kada yayi kasa da 140.

Karanta wannan  Rundunar sojin sama ta babbaka 'yan bindiga a mabuyarsu dake jihar Niger

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.