Jihar Kogi ta zama jihar ta 3 da ta bayyana cewa zata bude makarantun jihar ta a wannan watan na Satumba. A baya mun ji cewa jihohin Legas, da Osun suma sunce zasu bude makarantun masu.
Hakan na zuwa duk da shawarar da gwamnatin tarayya ta hannun sakataren gwamnatin, Boss Mustapha ta bayar na cewa bude makarantun ka iya dawo da cutar Coronavirus/COVID-19.
Kwamishinan Ilimi na jihar Kogi, Mr. Wemi Jones ne ya tabbatar da haka a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a yau, Talata.
Yace sun dauki matakanne bayan tuntubar masana da kuma duba yanayin makarantun. Yace duka makarantun jihar daga Firamare zuwa Jami’a ne za’a bude.