Babbar kotun tarayya dake Abuja ta soke karar da aka shigar akan mutane 119 kan zargin cib amanar kasa da shiga zanga-zanga.
Mai Shari’a Obiora Egwuatu ne ya soke tuhumar bayan da lauyan gwamnati MD Abubakar ya bukaci hakan.
A zaman kotun na yau Talata lauyan gwamnatin ya ce babban lauya na kasa ne zai ci gaba da kula da lamarin.