Daga Comrd Ibrahim Da’u Dayi
Ɗan takarar majalisar jiha a karamar hukumar Bakori Lawan Ahmad ya bayyana dakatar da tsayawarsa takarar a shekarar 2023
Jarumi kuma producer Lawan Ahmad sannan kuma dan takara ya bayyana cewa ya fasa tsayawa takarar kujerar da yake nema ta ɗan Majalisar jiha.
Jarumin ya bayyana dalilinsa na janye takarar inda ya rubuta kamar haka a shafinsa na Facebook.
“Na haƙura da takara sakamakon iyayenmu sunce mubari, kuma munbari shiyasa kukaji shiru kuma indai mutum yana so ya gama da duniya lafiya to yabi iyayensa”
Ya kuma jaddada cewa har yanzu yana nan a cikin jam’iyyar Apc, kuma zaici gaba da bada gudummawar sa iya bakin ƙoƙari.