Majalissar wakilai ta jihar Oyo ta tsige mataimakin gwamna, Rauf Olaniyan a yau ranar litinin.
Majalissar ta tsige shine saboda tace baua gudamar ayyukan da suka rataya a wuyansa yadda ya kamata kuma ana zarginsa akan aikata wasu abubuwa na daban.
A kwanakin baya mataimakin gwamnan ya maka majalissar a babban kotun jihar, amma kotun tayi watsi da karan tace suna da damar tsige shi akan mulki.
A shekarar 2019 ne Rauf Olaniyan ya lashe zaben tare da Uban gidansa Seyi Makinde a jam’iyyar PDP kafin daga bisani ya koma APC.