fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Yanzu-yanzu: Mawakin da ya kirkiri da fara rera taken matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC Anthem) ya rasu

Mawakin da ya kirkiri da rera wakar bautar kasa (NYSC anthem) Dr Oluwole Adetiran ya rasu.

Ya rasu ranar Juma’a 6 ga Mayu, 2022 yana da shekaru 74.

Mambobin cocin Celestial Church of Christ (CCC) da yawa sun tabbatar da mutuwarsa, wanda ya kasance memba.

Ko’odinetan NYSC na jihar Ogun, Dokta Belinda Faniyi, ita ma ta tabbatar da hakan, inda ta bayyana cewa tana shirin sanar da Darakta Janar din labarin.

Mawakin ya yi waƙar a 1984, ya ce ya ji daɗin cewa ana tuna da shi tun shekaru 37 da suka gabata bayan ya yi waƙar. Ya yi wakar ne a shekarar 1984 a lokacin da ya ke yi wa kasa hidima a jihar Oyo.

Karanta wannan  Ku fadawa Safara'u idan ta amince zan aure ta - Wani matashi

Ya koka da cewa yana fama da cututtuka da suka hada da hauhawar jini da ciwon suga da kuma cutar kansa tun a shekarar 2018.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.