Rahoto daga kafar Daily Mail ya tabbatar da Cewa, dan wasan Kasar Argentina me bugawa kungiyar PSG wasa, Lionel Messi ya amince ya koma kungiyar Alhilal ta kasar Saudiyya.
Hakan na nufin cewa, gasar dake tsakaninsa da Cristiano Ronaldo ta dawo sabuwa, kasancewar Cristiano Ronaldo din yana bugawa kungiyar Alnasr wasa.
Itama kafar AFP ta tabbatar da wannan labari inda tace wata majiya dake kusa da wannan lamari ta tabbatar mata da cewa a kakar wasa me zuwa, Messi zai buga wasa a Saudiyya.