fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Yanzu-Yanzu: Miliyan 100 iyalan shugaban bankin BOA suka biya kudin fanda kamin aka sakeshi

Jaridar Daily Nigerian ta fallasa cewa Miliyan 100 iyalan shugaban bankin BOA da ‘yan Bindiga suka kama suka biya a matsayin kudin fansa kamin aka sakeshi.

 

Alwan Hassan wands yana daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa dasu bayan harin da aka kaiwa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya samu kubuta.

 

Saidai ‘yan Bindigar sun ce wai saboda Azumin watan Ramadanane da kuma tsufansa yasa suka sakeshi, to ashe karyane.

 

Majiyar Daily Nigerian ta bayyana cewa duk da ‘yan Bindigar sun ce wai ba kudi suke nema ba, amma wata majiya tace saida suka biya Miliyan 100 aka sakeshi.

 

Hakanan kuma, kamin a sakeshi saida suka rika nuna musu bidiyonsa da sauran mutanen da aka sace cikin wani mummunan hali, Alwan ya rika cewa a basu ko nawa suke bukata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *