Friday, May 29
Shadow

Yanzu-Yanzu: Na bi shawarar gwamnati, na fasa bude guraren Ibada da Kasuwa>>Gwamnan Benue

Gwamntin jihar Benue ta bayyana cewa ta fasa bude guraren Ibada da kasuwanni kamar yanda ta bayyana a baya.

 

A ranar Alhamis din data gabatane, gwamnatin jihar ta bayyana cewa zata bude kasuwanni da kuma guraren Ibada da suka shafe kusan watanni 2 a kulle.

Saidai a sanarwar da gwamnatin ta fitar a yau, Asabar tace bisa ga shawarar da gwamnatin trayya ta bayar kan sake tunani gane da bude guraren Ibada ta fasa bude guraren ibadarta da kasuwar.

 

Jihar Benue dai na daya daga cikin jihohin da basu da masu cutar Coronavirus/COVID-19 da yawa inda hukumar NCDC ta bayyana cewa mutane 5 ne kawai aka samu da cutar a jihar

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *