Gwamnatin Najeriya ta aike da sojoji 173 zuwa kasar Guinea Bissau dan samar da zaman lafiya.
Jami’in sojin Najeriya, Major General Oluwafemi Akinjobi, ne ya bayyana haka a jaji Kaduna ranar Alhamis.
Ya bayyana hakane bayan hiras da sojojin da za’a aika aikin samar da zaman lafiyar.
Shima jami’in sojin Major General Zakari Abubakar, ya gargadi sojojin da cewa su tabbatar sun bi doka da oda wajan samar da zaman lafiya a kasar da aka turasu.