Hukumar yaki da sha da hana fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ta gani kwayar Biliyan 22 a hannun wanda ake zargi da yin safarar gwayoyi da shahararren dansanda Abba Kyari.
Rahoton yace a cikin wata daya Chief Afam Mallinson Ukatu ya shigo da wannan kwayar Najeriya.
NDLEA ta fitar da wannan sanarwar ne a yau, Laraba, 3 ga watan Mayu dan ta kawar da shakkun da wasu suke cewa bata da shaidar kama Chief Afam Mallinson Ukatu.
Sanarwar ta kara da cewa, Ukatu shine babban me shigo da kwayar Tramadol Hydrochloride Najeriya.
Kakakin hukumar NDLEA, Femi Baba Femi ne ya sanar da haka.