Jam’iyyar PDP ta karyata rade-raden da ake na cewa kwamitin data kafa din zabarwa Atiku abokin takara ta zabi gwamnan Rivers, Nyesom Wike.
Inda shugaban kwamitin, Debo Ologunagba ya bayyana hakan yau ranar laraba a jihar Abuja cewa labarin kanzan kurege ne cewa sun zabi Wike a matsayin mataimakin Atiku.
Kuma ya kara da cewa har yanzu suna nan su fafutukar zabar mutumin dayafi cancanta ya zama abokin takarar Alhaji Atiku Abubakar.