Ana can jam’iyyar APC ba zaman lafiya bayan da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana kakakin majalisa, Sanata Ahmad Lawal a matsayin zabin da aka yi wanda ba sai an yi zabeba ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar tasu.
Adamu ya bayyana hakane a wajan taron kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC dake gudana a Abuja.
Saidai yace duk da zabin na Ahmad Lawal sauran ‘yan takarar zasu iya tsayawa a fafata a zaben fidda gwanin.
Yace ya zabi Ahmad Lawal ne bayan tuntubar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.