Rahotanni sun bayyana cewa sanatocin APC 2, Sanata Yahaya Abdullahi da Adamu Aliero sun koma jam’iyyar PDP.
Kamfanin Dillancin labaran Najariya, NAN ya bayyana cewa Sanatocin sun sanat da kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal komawarsu PDP ne a wata takarda da suka aike masa a zaman majalisar na ranar Talata.
Duka sanatocin sun fito ne daga jihar Kebbi.
Akwai kuma sanata Enyinnaya Abaribe da shi kuma ya koma jam’iyyar APC daga PDP.