fbpx
Saturday, December 3
Shadow

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawa da fasinjojin jirgin kasa da suka samu ‘yanci daga hannun ‘yan bindiga

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na ganawa da iyalan fasinjojin jirgin kasa da suka samu ‘yanci daga hannun ‘yan bindiga.

Shugaba Buhari na ganawa da su ne a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja, biyo bayan wa’azin da Sheik Ahmad Gumi yawa ‘yan bindigar suka sako su.

A ranar 28 ga watan Maris na wannan shekarar ne ‘yan bindigar suka kaiwa jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja hari sukayi garkuwa da guda 65.

Wanda ‘yan bindigar ke sako su kashi kashi kuma a kwanakin baya sun saki wani bideyo suna lallasar su.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *