fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari, Osinbajo, Gwamnoni sun halarci taron Majalisar Zartarwa ta APC

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu, gwamnoni da sauran jiga-jigan jam’iyyar sun halarci taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar karo na 11.

Sauran wadanda suka halarci taron akwai shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan; mataimakinsa Sanata Ovie Omo- Agege; Femi Gbajabiamila; mataimakinsa, Hon. Idris Ahmed Wase da mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC).

Da yake maraba ’yan kwamitin, Adamu, ya gargadi jam’iyyar kan rashin hadin kai, yana mai cewa hakan a bayyane yake a jam’iyya mai mulki.

Karanta wannan  Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya rasa tikitin PDP a hannun mutumin Wike, ya zargi ‘yan jam'iyyar da yi masa taron dangi

Shugaban ya kuma ja kunnen ‘ya’yan jam’iyyar da su yi watsi da tunanin cewa za su iya faduwa zabe a 2023.

Ya tunatar da ‘yan jam’iyyar abin da ya samu jam’iyyar adawa ta PDP a 2015 saboda rashin hadin kai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.