fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Yanzu Yanzu shugaba Buhari ya umurci majalissar dattawa ta kaddamar da Alukayode Ariwoola a matsayin alkalin alkalai

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci majalissar dattawa cewa ta kaddamar da Alukayode Ariwoola a matsayon alkalin alkalai.

A safiyar yau ranar talata shugaban sanatoci, Ahmad Lawal ya karanta wasikar a majalissar dattawan dake babban birnin tarayya Abuja.

Ariwoola ya kasance alkalin alkalai na rikon kwarya tun bayan da Muhammad Tanko yayi murabus, kuma yanzu shugaban kasa ya nemi a kaddamar dashi.

Muhammad Tanko yayi murabus ne bayan manyan alkalai guda 14 sun yi zanga zanga cewa zasu tafi yajin aiki idan har ba a tsige shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.