fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Yanzu Yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ragamar kamfanin NNPC ga ‘yan kasuwa

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya mika ragamar kamfanin man Najeriya na NNPC ga ‘yan kasuwa.

Shugaban a taron da suka gudanar yau da safenan wanda aka fara da misalin karfe tara ne ya mika ragamar man fetur din ga ‘yan kasuwar.

Kuma yace yayi hakan ne don habaka tattalin arzikin kasa Najeriya kuma za’a ga cigaba sosai kan wannan gagarumin taron da suka gudanar.

Shugaban kasar ya mika sakon gaisuwarsa ga shugaban sanatoci Ahmad Lawal da sauran ministocinsa da gwamnanoninsa da suka hallaci wannan gagarumin taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published.