fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya zabi wanda zai masa mataimaki

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa ya zabi wanda zai masa mataimakin shugaban kasa.

 

Tinubu ya bayyana cewa amma ba zai bayyana sunansa ba tukuna sai nan gaba.

 

A jiyane dai Tinubu ya kaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyarar godiya bayan zaben fidda gwani na APC.

 

Hakanan Tinubun ya ziyarci ofishin mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo wanda suka yi takarar neman tikitin shugaban kasar tare.

 

Tinubu ya bayyana cewa, zai dora daga inda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tsaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.