fbpx
Saturday, March 25
Shadow

Yanzu-Yanzu: Wasu ‘yansandan Najeriya sun tsayar da ranar yin Zanga-Zanga saboda danne musu hakkokinsu

‘Yansandan Najeriya masu karamin mukami sun tsayar da ranar 1 ga watan Mayu a matsayin ranar da zasu fara yin Zanga-Zanga kan hakkokinsu da ake danne musu.

 

‘Yansandan dai zasu fara Zanga-Zangar ne saboda rashin kyawun yanayin aiki da Albashi da kuma rashin makamai na zamani.

 

‘Yansandan sun kuma koka da kashe abokan aikinsu da ‘yan Bindiga suke yi ba tare da ana biyan iyalansu hakkokinsu ba.

 

Sahara Reporters tace, ‘yansandan sun zargi gwamnatin Najeriya da musu karyar karin Albashi da kuma rashin samar da kayan aiki na zamani.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *