‘Yan Bindiga da anw zargin ‘yan IPOB ne sun afkawa motar sojojin Najeriya a jihar Abia.
Lamarin ya faru da safiyar yau, Juma’a a Tonimas junction, Karamar hukumar Osisioma.
Sojojin na rangadi ne, ba tsammani sai ‘yan Bindigar suka afka musu, sun dai kona motar sojojin amma babu cikakken bayanin ko an samu kisan mutane kamar yanda The National ta ruwaito.