Yanzu-yanzu
‘YAN BINDIGA SUN FAR WA ZAƁEN FID DA GWANIN SANATAN APC A NASARAWA TA YAMM
An ji ƙarar harbe-harbe a wurin zaɓen fidda gwani na Sanatan Nasarawa ta Yamma tsakanin Arc. Shehu Tukur da Barista Labaran Magaji a karkashin Jam’iyyar APC.
Wakilinmu, Zubairu Kawai ya aiko mana da cewa Tun wajen misalin ƙarfe 5 na yamma ake kiki-kaka a kan sauya jerin Daliget masu zaɓe wanda aka kasa samun daidaito.
Ana gudanar da zaɓen ne a Harabar Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi.
Babu dai wani labarin ko an rasa rai ko jikkata wasu zuwa rubuta wannan labarin.