fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Yanzu Yanzu ‘yan bindiga sun kashe inspectan ‘yan sanda na jihar Ondo

A safiyar yau ranar litinin ‘yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda dake Okuta a babban birnin jihar Ondo, wato Akure.

Inda ‘yan bindigar sukayi musayar wuta da jami’ai a ofishin nasu har suka harbi inspecta Temenu Boluwaji ya mutu yayi da ake hanyar kaishi asibiti.

Kuma mafi yawancin ‘yan sanda duk sun samu raunika sakamakon musayar wutar da sukayi da ‘yan bindigar, kuma hukumar ta tabbatar da wannan harin.

Inda ta bayyana bacin ranta kan harin da suka kai musamman saboda kashe babban jami’inta da sukayi, amma tace ba zata barsu ba domin an fara neman su domin a hukunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.