fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Yanzu-Yanzu: ‘Yan Bindiga sun kashe shugaban APC a jihar Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan Bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar na mazabar Mr.Iliya Auta dake karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

 

Rahoton daga Vanguard ya bayyana cewa, ‘yan Bindigar sun kai harinne ranar Litinin da dare inda suka kashe wasu mutane da jikkata karin wasu.

 

Hukumar ‘yansandan jihar dai bata ce komai ba kan lamarin amma shaidu sun tabbatarwa da jaridar faruwar hakan.

 

‘Yan Bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu mutane tare da sace wasu dabbobi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Biyo bayan kuma batanci ga annabi a bauchi rikicin addini ya kaure

Leave a Reply

Your email address will not be published.