‘Yan Bindiga sun sace Fulani 10 a jihar Anambra.
Sun kuma nemi a biyasu kudin fansa Miliyan 4 da Bindigar AK47 kamin su saki ‘yan Bindigar.
Lamarin ya farune a Obene dake karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah a yankin kudu masu gabas, Alhaji Gidado Siddiki ne ya tabbatarwa da manema labarai hakan.
Yace wadanda aka sace an sacesune tare da dabbobi inda ya roki wanda suka sace su din da su sakesu.