Rahotannin da muke samu na cewa, an garzaya da Aminu Muhammad zuwa fadar shugaban kasa dake Abuja bayan sakinsa daga gidan yarin Kuje.
Hakanan rahoton da ya fito daga jaridar Leadership na cewa, Aminu zai gana da shugaba Buhari.
Bayan ganawar tasune dai ake sa ran za’a sakeshi ya koma ga danginsa.