Rahotanni daga kasar Mali na cewa ciwon mutuwar rabin jiki ta kama hambararren shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa likitan Shugaban ya gaya musu ciwon ba mai tsanani bane amma alamace dake nuna cewa nan gaba me tsananin zai iya kama shugaban.
A baya dai wani hadimin shugaban ya bayyana cewa an kwantar dashi a Asibiti kuma za’a sallameshi a yau dan kawai ya je a duba lafiyarsa ne amma daga baya kuma sai aka bayyana cewa za’a ci gaba da dubashi har abinda hali yayi.
Sojojin da suka hambarar dashi dai sun bayyana cewa idan akwai bukatar ya fita kasar waje neman lafiya zasu bashi damar hakan.