fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Yanzu-Yanzu:Coronavirus/COVID-19 ta kashe mutum na farko a kasar Madagascar

Rahotanni dake fitowa daga kasar Madagascar na cewa cutar Coronavirus/COVID-19 ta kashe mutum na farko me shekaru 57 a garin Toamasina dake kasar.

 

Me magana da yawun kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 a kasar, Hanta Vololontiana ne ya tabbatar da haka a yau,Lahadi inda yace mutumin ya mutune a jiya, Asabar.

 

Hakanan akwai karin mutane 2 da suke a wajan kulawa na musamman game da cutar ta Coronavirus/COVID-19.

 

Kasar ta samu karin mutane 21 da suka kamu da cutar a yau, Lahadi, kamar yanda kamfanin dilkancin labaran kasar, MPA ya ruwaito.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Yanzu kasar nada mutane 304 da suka kamu da cutar.

 

A baya dai ansha dambarwa da kasar ta Madagascar inda ta yi ikirarin cewa ta samu maganin cutar Coronavirus wanda hukumar lafiya ta Duniyw, WHO bata yi na’am dashi ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.