Wasu mutane daga kauyen ‘Yangayya a jihar Katsina sun fito tsakiyar Titi wanda ya hada Garin Katsina da Jibia suka tare hanya inda sukace ba zasu bude ba sai gwamnati ta musu maganin harin ‘yan ta’adda da suka addabesu.
Masu zanga-zangar sun sa matafiya da dama tsayawa saboda babu hanyar wucewa.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa, kauyawan sun zargi Maharan da musu Fyade da Satar mutane dan kudin fansa.