fbpx
Thursday, July 2
Shadow

Yanzu-Yanzu:Shugaba Buhari ya sake nada Umar Danbatta matsayin shugaban hukumar sadarwa ta NCC

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Umar Danbatta a matsayin hmshugaban hukumar Sadarwa da NCC a karo na 2.

 

Shugaba Buhari ne dama ya nada Danbatta wanda Farfesa ne a fannin Kimiyyar Sadarwa shekaru 4 da suka gabata a kan mukamin.

Me magana da yawun ma’aikatar Sadarwa da tattalin arzikin zamani,Uwa Sulaiman ce ta bayyana haka a sanarwar data fitar me sa hannun ministan ma’aikatar, Dr. Isa Ali Pantami.

 

Pantami ne ya bayar da shawarar sake nada Danbatta akan wannan mukami wanda kuma shugaba Buhari ya amince da wannan shawara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *