Kungiyar Boko Haram ta afkawa garin Bama dake jihar Borno da yammacin yau.
Saidai sojojin Najeriya sun tare kungiyar inda yanzu haka ana can ana bata kashi tsakaninsu a wajen garin.
Hakanan, Boko Haram da yawa sun kashe sojoji biyu a wani gari me suna Molai dake kusa da birnin Maiduguri, kamar yanda Zagazola ya ruwaito.