Rahotanni daga Maiduguri jihar Borno na cewa, an samu fashewar bam a birnin yayin da ake dakon isowar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Rahoton wanda ya fito daga HumAngle ya bayyana cewa, bam din ya tashine da safiyar yau da misalin karfe 10:45.
Inda bam din ya tashi bai da nisa da filin jirgin sama na Maiduguri, kamar yanda majiyar ta ruwaito.
Wasu daga cikin shaidu sun bayyana cewa, an cillo bam dinne daga nesa wanda ya fada gidan mutane ya kuma kashe wasu da ba’a kai ga tantance yawansu ba.
Hakanan an cilla bam na 2 cikin wani gidan biredi wanda shima ya jikkata mutane