Kungiyar malaman jami’a da aka fi sani da ASUU ta bayyana cewa zata ci gaba da yajin aikin da take har nan da makwanni 12.
Ta bayyana hakane bayan ganawar da suka yi ta tsawon lokaci a tsakaninsu.
Shugaban kungiyar, Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa, sun dauki wannan mataki ne dan baiwa gwamnati isashshen lokaci ta magance matsalar.