Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta kammala yajin aikin gargadi da take.
Kungiyar ta dauki yajin aikin makwanni 8 wanda zai kare ranar litinin me zuwa. Amma ana tsammanin zasu ci gaba dana dindindin.
A ranar litinin ake tsammanin ASUU zasu fitar da matsayinsu akan yajin aikin.
Ministan kwadago, Chris Ngige yace zasu tattauna da kungiyar ASUU dan magance matsalar yajin aikin.
Amma ASUU na zargin gwamnati da yin wofi da maganar bukatunsu.